Artv News
Calvin Ramsay: Aberdeen ta amince da tayin da Liverpool ta yi wa matashin Scotland

Aberdeen ta sallama tayin fam miliyan 4.5 da Liverpool ta yi wa matashin dan wasa, Calvin Ramsay mai shekara 18.
Cikin kunshin kwantiragin zai hada da karin tsarabe-tsarabe na fam miliyan uku da karbar kaso 20 cikin 100, idan kungiyar Anfield za ta sayar da shi.
Dan wasan tawagar Scotland ta matasa 'yan kasa da shekara 21, ya amince da yarjejeniyar kaka biyar, ana sa ran zai kammala cimma kwantiragin da zarar likitoci sun gama auna koshin lafiyarsa.
Hakan ya zama na farko da Aberdeen ta sayar mafi tsada a tarihinta, bayan mai tsaron baya Scott McKenna da ya koma Nottingham Forest a 2020 kan fam miliyan uku.
Ramsay ya yi wasa 39 a kungiyar har da 33 a kakar da aka kammala a Aberdeen, wadda ya fara tun daga matakin reno.Mai tsaron baya daga tsakiya, shi ne matashin shekara da marubuta labarin wasanni na Scotland suka karrama a cikin watan Afirilu, duk da cewar kungiyar ta karkare kakar da ta wu ce a mataki na 10 a teburi.
Idan kungiyar Anfield ta kammala cinikin dan kwallon zai zama na uku da Liverpool ta dauka a bana, bayan Darwin Nunez daga Benfica kan fam miliyan 64 da Fabio Carvalho daga Fulham kan fam miliyan biyar.
BBC