top of page
  • Writer's pictureArtv News

Buhari Zai Ciyo Bashin N402bn Domin Biyan Bashi


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na neman amincewar Majalisar Dattawa domin ciyo bashin Naira biliyan 402 da zai yi amfani da su wajen biyan bashi.


Buhari ya bayyana haka ne a wasikar da ya aike wa Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan a ranar Talata.


Ya bayyana cewa za a karbo bashin ne ta hanyar bayar da takardun lamuni domin samun kudaden da za a biya bashin Naira biliyan 375da masu fitar daga kaya daga Najeriya suke bin Gwamnatin Tarayya.


Za kuma a yi amfani da kudaden wajen biyan jihohin Yobe Kebbi da Taraba kudadensu da suka kashe wajen gyaran titunan Gwamnatin Tarayya.


Daga cikin takardun lamunin Buhari ke sa ran samun kudin da zai biya Gwamnatin Jihar Yobe biliyan N18.623 da ta kashe wajen tituna biyar na Gwamnatin Tarayya a Jihar

Ofishin Kula da Basuka na Kasa (DMO) ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kebbi ta kashe biliyan N6.706 a yayin da Gwamnatin Taraba ta kashe biliyan 2.706 wajen gyaran titunan Gwamnatin Tarayya.


Hakan kuwa na zuwa ne a ranar da DMO ta bayyana cewa yawan basukan da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 42, bayan kasar ta ciro karin bashin Naira biliyan uku a cikin wata uku (Maris zuwa Yuni 2022).


A halin yanzu basukan da ake bin kasar sun ninka kasafin kudin 2023 na Najeriya sau biyu.

Idan aka raba wa ’yan Najeriya mutum miliyan 200 bashin, kowannensu zai biya Naira 210,000.

(AMINIYA)

37 views0 comments
bottom of page