top of page
  • Writer's pictureArtv News

Buhari ya saka tubalin ginin sabuwar hedikwatar Ecowas

Shugaba

Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da tubalin ginin sabuwar hedikwatar Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas a Abuja babban birnin ƙasar.


Shugabannin ƙasar Guinea Bissau Umaro Embaló, da na Saliyo Julius Maada Bio, da Shugaban Ecowas Omar Alieu Touray, da Jakadan China a Najeriya Cui Jianchun, su ne suka taya Buhari saka ɗambar ginin a yau Lahadi.


Ana sa ran kammala sabuwar hedikwatsar a shekara ta 2025.


Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana cewa hamshaƙin ginin, wanda gwamnatin China ta samar da kuɗin ginawa, zai ƙarfafa zumunci a tsakanin ƙasashen Afirka.


BBC Hausa ta rawaito cewa, Ginin zai kuma wakilci al'ummar Afirka ta Yamma mutum miliyan 380 sannan zai kasance matsuguni ga manyan cibiyoyin Ecowas uku, ciki har da ginin hukumar gudanarwar ƙungiyar da Kotun Ecowas, har ma da Majalisar Dokokin Ecowas.


A gefe guda kuma, shugabanin mambobin ƙungiyar na gudanar da taro karo na 62.



1 view0 comments
bottom of page