top of page
  • Artv News

Buhari ya nada sababbin ministoci


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sababbin ministoci domin maye gurbin wadanda suka sauka da wadanda ya sauke daga kan mukamansu.


Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmed Lawan ne ya karanto sunayen sababbin ministocin da Shugaba Buhari ya aike wa majalisar a zaman da ta yi ranar Talata.


BBC Hausa ta rawaito cewa, Sabbin ministocin sun hada da Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano, Umana Okon Umana (Akwa Ibom), Henry Ikechukwu Iko (Abia), Ademola Adegoroye (Ondo), Odum Odi (Rivers).

Sauran su ne Goodluck Nnana Opia (Imo) da kuma Joseph Ukama (Ebonyi ).


Sanata Lawan ya ce nan gaba za su tantance ministocin da aka mika musu domin tabbatar da su ko kuma akasin haka.

A watan Satumbar 2021 ne Shugaba Buhari ya sauke Ministan harkokin Gona, Alhaji Sabo Nanono da Ministan Ma'aikatar Lantarki, Injiniya Saleh Mamman ba tare da bayyana wani dalili ba.


Kazalika a watan jiya ya umarci ministocinsa da ke son tsayawa takarar siyasa su sauka daga mukamansu.

103 views0 comments
bottom of page