top of page
  • Writer's pictureArtv News

Buhari ya kai ziyara gidan yarin Kuje kafin ya wuce Senegal


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yanzu haka yana can yana ziyara a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja don gane wa idanunsa irin barnar da mahara suka yi, gabanin ya wuce kasar Senegal.


A daren Talata ne dai ’yan bindiga suka kai hari gidan tare da sakin fursunonin sama da 800, ciki har da mayakan Boko Haram.


Aminiya ta rawaito cewa Fadar Shugaban Kasa ta sanar da cewa Buhari na kan hanyarsa ce ta zuwa kasar Senegal domin halartar wani taro na Bankin Duniya a Dakar, babban birnin kasar.


Lamarin dai ya jawo suka iri-iri, inda mutane ke cewa sam Shugaban bai damu da matsalar tsaron da ta addabi kasar ba.


Tawagar Buharin dai ta isa gidan ne wajen misalin karfe 3:30 na yamma, kamar yadda bayanai suka nuna.

6 views0 comments
bottom of page