top of page
  • Writer's pictureArtv News

Buhari ya dawo da Bashir Ahmad mukaminsa, tare da daga likafarsa


Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsohon mai taimaka masa kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, a matsayin Hadimi na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Sadarwa na Zamani.


Wannan dai na kunshe ne a cikin wata wasikar tabbatar da nadin da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya aike wa da Bashir mai dauke da kwanan watan ranar 20 ga Yulin 2022.


Cikin wasikar da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya gani, sabon mukamin da Buhari ya bai wa tsohon hadimin zai fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Yulin bana.


Ana iya tuna cewa, gabanin zaben fitar da gwanayen takara ne Bashir Ahmad ya yi murabus daga mukaminsa domin neman takarar dan Majalisar Wakilai na Kananan Hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu da ke Jihar Kano.


Wannan dai ya yi da da umarnin da Buhari ya bai wa duk hadimansa na ajiye mukamansu gabanin neman takarar wata kujerar siyasa.


Sai dai Bashir bai yi nasara ba, inda ya sha kaye a zaben fidda gwanin takarar, yana mai watsi da sakamakon zaben, wanda ya ce cike yake da rudani sakamakon rikicin da ya ce ya barke a wurin zaben.

97 views0 comments
bottom of page