top of page
  • Writer's pictureArtv News

Buhari ya baiwa Ministan Ilimi wa’adin mako 2 kan ya kawo ƙarshen yajin aikin ASUU


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu, mako biyu ya kawo karshen yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ke yi.

Buhari ya kuma umarci Ministan Kwadago, Chris Ngige, kada ya kuskura ya halarci zaman tattaunawar sulhu da gwamnati ta kira malaman jami’ar

Ya umarci Ministan Ilimin da ya jagoranci zaman da gwamnati ta gayyaci ASUU da nufin sasantawa da su da sauran kungiyoyin jami’o’i da ke yajin aiki.

Haka kuma majiyarmu ta bayyana mana cewa Buhari ya kuma umarni Adamu da ya tabbata an yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen yajin aikin kungiyar cikin mako biyu.

Karin bayani na tafe…

26 views0 comments
bottom of page