top of page
  • Writer's pictureArtv News

Buhari Ya Ba Da Umarnin Hukunta Sojan Da Ya Kashe Sheikh Goni Aisami


Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a hukunta sojan na da ake zargi da kashe Sheikh Goni Aisami bayan malamin ya rage masa hanya a motarsa a Jihar Yobe.


A sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Goni Aisami da Gwamnatin Jihar Yobe, Shugaba Buhari ya umarci hukumomin soji da su tabbata cewa sojan da duk wadanda suka taimaka masa sun ya girbi abin da aya shuka gami da kakkabe duk wani baragurbi a cikin sojoji.


Sanarwar da hadimin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar ta ce “Irin wannan kidahumanci na kashe mutum mai tausayi” da sojan ya yi ya saba duk wata koyarwa da kuma horo da aka san soja da shi.


A cewarsa, an san soja ne da bin doka da mutunci da kuma sanin martabar rayukan mutane.

“Horon da ake mana a matsayin sojoji shi ne na mu zama masu kamun kai da hakuri da kuma bin doka sau da kafa.


“Ba koyarwar soji ba ce cutar da mutane; Abin da wannan sojan ya aikata bako ne, amma yana barazana ga martabar rundunar tsaron kasar nan.


“Kisan Sheikh Goni Aisami da sojan ya yi zai iya sanya al’ummar kasar nan su razana da sojojinmu, wanda hakan ka iya wargaza yardarsu da sojojin,” in ji Buhari.


Buhari ya gaggauta hukunta makasa Sheikh Goni Aisami —JNI


A nata bangaren, Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ta bukaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin sojin Najeriya su gaggauta hukunta masu laifin kashe Sheikh Goni Aisami domin yi wa mamacin da iyalansa adalci da kuma taka wa bata-garin sojoji burki.


JNI ta kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki irin wannan mataki a kan duk inda aka samu jam’ian tsaro ko wani mutum ya yi irin wannan aika-aikan a fadin Najeriya.


Babban Sakataren Kungiyar JNI, Dokta Khalid Abubakar Aliyu, ya ce tabbatar da hukunta miyagu cikin jami’an tsaro zai sa su shiga taitayinsu.


A sanarwar da ya fitar, Dokta Khalid ya bayyana cewa bisa dukkan alamu wadanda suka kashe Sheikh Goni Aisami sun tsara yadda za su aiwatar da kisan ne, amma asirinsu ya tonu.


Ya ce irin haka ne ya faru a shekarar 2018 inda aka yi wa Manjo-Janar Idris Alkali kisan gilla a Jihar Filato aka kuma jefa gawarsa a wani kududdufi.


“Amma abin takaici, har yanzu babu abin da aka yi wa wadanda suka aikata laifin.


“Irin haka ne kuma ya auku a Hanyar Rukuba inda aka yi wa Musulmi matafiya 22 kisan gilla a hanyarsu ta dawowa daga Jihar Bauchi zuwa Ikare a Jihar Ondo bayan sun biyo ta Jos.


“Bugu da kari, an sha yi wa Musulmi irin wannan kisan gilla cikin ruwan sanyi ba tare da an hukunta masu laifin ba.


“Amma duk da haka al’ummar Musulmin kasar nan ba su dauki doka a hannunsu ba; duk kuwa da irin karairayin da ake yadawa gami da takalar su haka kawai,” in ji sanarwar ta JNI.


Ta kara da cewa kisan da aka yi wa malamim ya nuna yadda aikata manyan laifuka ya yadu a tsakanin ’yan Najeriya, ciki har da jami’an tsaro.


Gwamnatin Yobe ta dauki ’ya’yan Sheikh Goni Aisami aiki


Tuni dai Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ba da umarnin a dauki ’ya’yan malamin maza biyu aiki nan take.


Buni ya bayar da umarnin ne a lokacin da iyalan Sheikh Goni Aisami suka kai mishi ziyarar godiya bisa yadda ya nuna musu kulawa bayan kisan malamin.


Gwamnan, ta bakin kakakinsa, Mamman Mohammed, ya ce gwamnatin jihar za ta gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya kai ga kashe malamin, kuma za ta ci gaba da kulawa da iyalansa.


Malam Ibrahim Aisami, wanda ya yi jawabi a madadin iyalan Sheikh Goni Aisami ya ce aikin da gwamnan ya bai wa ’ya’yan malamin zai taimaka wajen rage kuncin rayuwar da rasuwar mahaifinsun za ta haifar.

(AMINIYA)

11 views0 comments
bottom of page