top of page
  • Artv News

Buhari, Fafaroma sun yi Allah wadai da harin Ondo

‘Yan bindiga a Najeriya sun kai wani kazamin hari a wata mujami’ar Katolika dake Owo a Jihar Ondo inda suka kashe mutane akalla 50, tare da raunata wasu da dama daga cikin su.

Rahotanni sun ce ‘Yan bindigar sun kai harin ne da safiyar yau a mujami’ar St Francis lokacin da ake gudanar da ibada, inda suka bude wuta akan mai uwa da wabi da kuma hallaka mutane da dama. Fafaroma Francis ya bayyana takaicin sa da harin wanda yayi sanadiyar hallaka mutane da dama cikin su harda kananan yara, yayin da yayi addu’a ga wadanda harin ya ritsa da su.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin da dalilin kai harin, yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kisan masu ibadar. Mai magana da yawun rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ibukun Odunlami tace ‘Yan bindigar sun fara kai harin ne da na’uran fashe fashe, abinda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Odunlami ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar ya zuwa yanzu babu cikakken adadin mutanen da suka mutu, amma kuma da dama daga cikin wadanda harin ya ritsa da su sun rasa rayukan su.

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa AFP cewar akalla mutane 20 sun mutu, yayin da wasu majiyoyi ke cewa adadin ya zarce 50.

Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bayyana harin a matsayin aikin shaidan, yayin da ya sha alwashin zakulo wadanda suka aikata domin ganin an hukunta su.24 views0 comments
bottom of page