Artv News
Boris Johnson zai sauka daga shugabancin jam'iyyarsa

Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai sauka daga shugabancin jam'iyyarsa ta Conservative a yau Alhamis.
Amma zai ci gaba da kasancewa firaministan kasar har zuwa watan Oktoba.
Za a naɗa sabon shugaban jam'iyyar Conservative a wannan bazarar sannan za a yi sabon firaminista a watan Oktoba ɗin.
Duk da cewa Boris Johnson bai kammala yin murabus ɗin ba a hukumance, har an fara kamfe kan wanda zai gaje shi.
BBC Hausa ta rawaito cewa, Zuwa an jima ne a ranar Alhamis Johnson zai sanar da murabus din nasa a hukumance.
Wani mai magana da yawaun fadar Gida Mai Lamba 10 ya ce: "Firaministan zai yi sanarwa ga ƴan ƙasar zuwa an ji ma."
Mr Johnson ya yi magana ne da Sir Graham Brady, shugaban kwamitin jam'iyyar Conservative na 1922 , inda ya sanar da shi matakin da ya ɗauka, a cewar wata majiya daga fadar No 10.
Majiyar ta ƙara da cewa: "Firaminsita ya yi magana da Graham Brady inda ya amince ya sauka a kan lokaci don ba da damar naɗa wani sabon shugaban a Oktoba."