top of page
  • Writer's pictureArtv News

Batun Cewa Atiku Zai Mayar Da Jami`O`In Tarayya Hannun Jihohi Ba Gaskiya Ba Ne —Paul Ibe


Paul Ibe, mashawarcin dan takarar shugaban kasa a jam’iyar PDP Atiku Abubakar, ya ce batun da wasu kafafen yada labarai a Najeriya ke yadawa cewa Atiku ya ce zai mayar da jami’o’in Gwamnatin Tarayya hannun gwamnatocin jihohi idan ya zama shugaban kasa a 2023 rashin sanin inda ya dosa ne.


Ibe, ta wata sanarwa ya ce da gangan kafafen suka yada labarin karyar, da suka ce dan takarar ya yi a jawabinsa ga taron Kungiyar Lauyoyin Najeriya karo na 62.


Ya ce, “Abin da dan takarar ya yi nuni da shi, shi ne shirinsa na rage karfin ikon Gwamnatin Tarayya zuwa ga gwamnatocin jihohi a bangarori da dama.

“Sai kuma batun da ya yi na cewa kasar Amurka ma ta taba yin makamancin wannan tsarin a wasu jami’o’in farko da ta kafa a Najeriya, inda ta mika ikon gudanarwarsu ga gwamnatocin jihohi.”


Ibe ya ci gaba da cewa, idan aka samar da kyakkyawan shiri, da kuma rage karfin iko kadan-kadan, jami’o’in Gwamnatin Tarayya da a yanzu ba ta iya gogayya da na Turai, za su bada abin da ake bukata.


“A jawabin nasa dai, Atiku ya ce ilimi zai ci gaba da kasancewa a jerin abubuwan da gwamnatinsa za ta fi bai wa fifiko idan aka zabe shi,” in ji Ibe.


“Ya kuma sake nanata matsayinsa kan yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ke yi, inda ya ce da zarar ya zamo shugabn Najeriya, gwamnatinsa za ta mai da hankali wajen kulawa da bukatun dalibai da malaman,” in ji Ibe.

(AMINIYA)

8 views0 comments
bottom of page