Artv News
Ba mu da wata matsala kan zaben Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu — Gwamnonin APC

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya na jam’iyyar APC sun musanta rade-radin da ake yi cewa ba su ji dadi ba da Bola Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.
Gwamnonin sun ce suna goyon zabin da aka yi wa Kashim Shettima dari bisa dari saboda shi ma tsohon gwamna ne.
A tattaunawarsu da BBC, gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce suna goyon bayan zabin kuma za su tsaya tsayin-daka wajen ganin jam’iyarsu ta kai gaci a zaben 2023.
Gwamnan na Gombe ya ce "Ai Kashim namu ne, kuma idan gwamna ne ya yi har ya wuce, kuma ba za mu ki Kashim ba saboda dalilai da dama.”
Ya ce: "Idan ka hada Asiwaju da Kashim din duk sun yi gwamna, sannan sun yi sanata, don haka sun taba duniyar biyu gabaki daya, don ba wanda za ka taba a cikinsu da ba shi da kwarewar da zai taimaka don a samu nasara da ci gaba.”
Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce su wannan ba shi ne damuwarsu ba. Abin da suke bukata shi ne jam’iyyar APC ta kai ga nasara.
Gwamnan na Gombe, "Mu Alhamdullih mun yarda da hukuncin Allah, kuma za mu yi aiki kamar yadda ya kamata don tabbatar dukkan gwamnoninmu na jam’iyarmu za su bayar da hadin kan da za a yi aiki har a kai ga nasara.”
Ya kara da cewa: “Batun cewa ba mu halarci taron kaddamar Kashim ba, tabbas ba dukkanmu ne muka halarta ba, kuma hakan ba wai na nuna cewa wasu daga cikinmu na da ja ba ne, saboda ko da nasara aka yi a zaben ma ba kowa ne a cikin gwamnonin zai samu damar halartar bikin rantsuwar ba.”
Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya ce babu wata damuwa a ciki, don ba a ji kuka daga bakin wani daga cikinsu ba.
A kwanakin baya ne dan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya zaɓi tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a takarar shugaban ƙasa.
Tinubu ya bayyana haka ne ga ƴan jarida a garin Daura yayin wata ziyarar barka da Sallah da ya kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Tun da farko dai tsohon gwamnan na Jihar Lagos ya ɗauki Ibrahim Masari a matsayin mataimaki duk da tun a lokacin ana ta ce-ce-ku-ce kan cewa na riƙo ne, kuma shi ma Masarin a yayin wata hira da BBC a kwanakin baya ya tabbatar da cewa a shirye yake ya bar kujerar idan aka samu wanda ya fi shi cancanta.
A halin yanzu Kashim Shettima ne sanata mai wakiltar yankin tsakiya na Jihar Borno.
Haka kuma ya bayar da muhimmiyar gudunmawa a yaƙin neman zaɓen Tinubu a lokacin zaɓen fitar da gwani na Jam'iyyar APC.