top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ba mu da sunan Ahmed Lawan da Akpabio a jerin 'yan takarar APC - INEC


Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta bayyana cewa Jam'iyya mai mulki a kasar, APC, ba ta da 'yan takarar Sanata a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.


Shugaban Majalisar Dattawan kasar, Ahmed Lawan, mai wakiltar Yobe ta Arewa na fafutukar samun tikitin tsayawa takara karkashin Jam'iyyar APC bayan da ya sha kaye a zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa.


Shi ma tsohon Gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, wanda ya fafata a zaben fitar da gwanin na kujerar Shugabancin Najeriya, na fuskantar wata turka-turkar ta neman sahalewar APC don samun damar wakiltar al'ummar mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a Majalisar Dattawa.


Sai dai Kwamishinan Hukumar zabe, Festus Okoye ya ce INEC ba ta da wani dan takarar APC da zai wakilci mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.


A wata hira da Gidan Talabijin na Channels TV, Okoye ya kara da cewa "a mazabun biyu, an gabatar da sunayen mutum biyu kuma hukumar ta yanke hukuncin cewa mutanen ba su ne halastattun wadanda suka lashe zaben fitar da gwanin da APC ta gudanar ba kuma ba mu wallafa sunayensu ba".


Ya ce APC ta dora sunayen Lawan da Akpabio cikin jerin sunayen 'yan takara a shafin intanet na INEC amma hukumar zaben ta yanke hukuncin cewa mutanen biyu ba su ne aka tsayar da su ba a zaben fitar da gwanin Jam'iyyar.


A cewar Okoye, rashin wallafa sunayen mutanen biyu da bayanansu a karkashin mazabun na nufin zuw yanzu APC ba ta da sunayen 'yan takarar a mazabun biyu.


Ko a makon da ya gabata sai da INEC ta musanta sauya kwanan watan wasu takardu domin samun damar shigar da sunayen Lawan da Akpabio a matsayin 'yan takarar kujerar Sanata a babban zaben kasar na 2023.


INEC dai ta bayyana cewa ba ta wallafa foma-foman mutanen biyu ba - matakin da ya sa aka shigar da kara wadda kuma har yanzu take gaban alkali.


Hukumar zaben ta ce hakan ne ya sa ta yi watsi da duk wata dabara ta gabatar da takardun bogi da ke tabbatar da takarar mutanen biyu a daidai lokacin da maganar ke gaban kotu.

(BBC HAUSA)

9 views0 comments
bottom of page