top of page
  • Artv News

Ba a samu fitina ba a zaben fitar gwani na Gwamnan Kano na APC – APC ta kasa

Jam’iyyar APC ta Kasa, ta ce babu wata hatsaniya da aka Samu Kan zaben fidda gwanin Gwamna Kano na Jam’iyyar.


Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Shugaban Matasan jam’iyyar na arewa masu yamma Abdulhamid Umar Muhammad ya sanyawa hannu Kuma aka aikowa Kadaura24.


Kadaura24 ta rawaito Sanarwar na cewa an

gudanar da Sahihi Kuma amintaccen zaben fidda gwani na kujerar Gwamnan Kano na Jam’iyyar APC


“Ofishina ya samu rahotanni daga dukkan jihohin nan bakwai Ina so in yi amfani da wannan dama don yabawa dukkan shugabannin jam’iyyar na jihohin, da wakilan Hukumar zabe Mai Zaman kanta ta kasa INEC wacce ta sa ido a kan dukkan zaben fidda gwanin”. Inji Shugaban Matasan


“Musamman game da Jihar Kano, kasancewarta ɗaya daga cikin jihohin da suka gudanar da zaben fidda gwani na gaskiya kuma mafi ingancin zaben gwamna a duk jihohin jam’iyyar APC”.


Jagororin jam’iyyar Kano sun taka rawar gani da kuma wakilan da suka gudanar da zaben ta hanya mai kyau.


Hakika zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamna a jihar Kano na daya daga cikin mafi kyawu an gudanar da zabukan ba kawai a shiyyar Arewa maso Yamma ba, har ma a duk fadin jihohin jam’iyyar APC a kasar nan.


WhatsAppFacebookTwitterTelegramShare

21 views0 comments
bottom of page