top of page
  • Writer's pictureArtv News

Arsenal ta tsawaita zaman Saka, Kounde ya koma Chelsea daga Sevilla



Arsenal ta yi wa Bukayo Saka, dan wasan gaba mai shekara 20 tayin sabuwar kwantiragi mai dogon zango, matakin da zai ribanya albashinsa domin hana kungiyoyi kamar Manchester City yin awon-gaba da shi.


Chelsea ta sha gaban Barcelona wajen dauko Jules Kounde, dan wasan baya mai shekara 23 daga Sevilla inda zai sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Stamford Bridge.


Kocin Ajax Alfred Schreuder ya ce dan wasan gefe na Brazil Anthony mai shekara 22 zai yi zamansa a kungiyar duk da cewa Manchester United ta so raba shi da kungiyar.


Chelsea da Tottenham sun nuna sha'awar sayen Allan Sanint-Maximin, dan wasan gefe na Newcastle United mai shekara 25.

Liverpool kuwa na neman karin bayani kan Jude Bellingham, dan wasan tsakiya na Ingila da Borussia Dortmund a watan Yuni sai dai kungiyarsa ta Jamus ta ki amincewa ta rabu da dan wasan mai shekara 19.


Da alama dan wasan gaba na Barcelona da Netherlands Memphis Depay mai shekara 28 zai ki amincewa da tayin da akai masa na komawa Newcastle.


West Ham na daf da sayo Gianluca Scamacca, dan wasan gaba mai shekara 23, bayan da ta amince da tayin fam miliyan 30.5 da Sassuolo ta yi ma ta.


Dan wasan baya na Leicester City Luke Thomas mai shekara 21 na iya komawa West Ham.


Arsenal da Everton sun ki amincewa da damar da aka ba su ta sayo Thomas Lemar, dan wasan gefe na Atletico Madrid da Faransa.


BBC HAUSA

11 views0 comments
bottom of page