top of page
  • Writer's pictureArtv News

APC ta fada sabon rudani bisa amincewa da Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na 'sulhu


Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fada cikin sabon rudani bayan shugabanta, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa sun amince da shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa.


Bayanai sun nuna Sanata Adamu ya bayyana haka ne a wurin taron kwamitin gudanarwa na

jam'iyyar ta APC a Abuja ranar Litinin din nan.


Ya sanar da wannan mataki ne kwana guda kafin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.


Sai dai jim kadan bayan hakan, gwamnonin Jihohin arewacin Najeriya karkashin jam'iyyar APC sun yi watsi da matsayar shugaban jam'iyyar tasu.


Daya daga cikin gwamnonin ya shaida wa BBC cewa suna nan a kan bakansu na mika mulki ga bangaren kudancin kasar a zaben 2023.


Rahotanni sun nuna cewa Sanata Abdullahi Adamu ya shaida wa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta APC matsayarsu ne bayan ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari.

37 views0 comments
bottom of page