top of page
  • Writer's pictureArtv News

APC: Kashim Shettima ya nemi afuwar Osinbajo da Ahmad Lawan kan kalaman da ya yi a kansu


Tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya nemi afuwar Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo bisa kalaman muzantawa da ya yi a kansa.


Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi, Sanata Shettima ya kuma nemi afuwar Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Ahmed Lawan, shi ma bisa kalaman da ba su dace ba da ya yi a kansa.


A ranar Alhamis da ta wuce ne tsohon gwamnan na Jihar Borno ya bayyana cewa Farfesa Osinbajo mutum ne mai kirki, "amma mutanen kirki ba su dace da shugabanci ba sai sayar da gurgugu da askirim (ice cream).

Kazalika, ya bayyana cewa duk da yake shugaban majalisar dattawan dan yankinsu ne amma babu wanda ya san shi a Najeriya, yana mai cewa hasali ma idan aka ambaci sunan Ahmad Lawan a yankin kabilar Igbo, mutummin da zai zo musu a rai shi ne "mai sayar da tumatur".


BBC ta rawaito cewa ya yi wadannan kalamai ne yayin da yake jaddada muhimmancin ganin jam'iyyar APC ta tsayar da tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a zaben 2023.


Sanata Shettima na ganin shi ne kadai yake da "karbuwa sannan aka san shi a fadin Najeriya" a cikin masu son yi wa jam'iyyar takara.


'Ba a fahimci kalamaina ba'


Sai dai a sakon da ya wallafa a Tuwita, Sanata Shettima ya ce yayin tattaunawarsa da gidan talbijin na Channels bai yi niyyar "muzanta kowanne dan takara ba, ballatana abokaina da abokan shawarata."


"Duk cikinsu babu dan hamayya don haka bukatarsu ta tsayawa takara ba barazana ba ce a gare mu," in ji tsohon gwamnan na Jihar Borno.


Sanata Shettima ya kara da cewa an zuzuta kalaman da ya yi a kan Osinbajo da Ahmad Lawan kuma ba a fahimce su ba.


"Ban yi kalamaina domin na nuna su a matsayin wadanda ba su dace su yi takara ba, sai don kawai na nuna cewa su ba barazana ba ne a gare mu," in ji Kashim Shettima.


Ya kara da cewa "duk da haka ina neman afuwa ga mataimakin shugaban kasa da shugaban majalisar dattawa bisa radadin da wadannan kalamai nawa - da na yi ba da niyya ba - suka haddasa a gare su da iyalansu da kuma magoya bayansu."

27 views0 comments
bottom of page