top of page
  • Artv News

Ana son yin sako-sako da batun nuna wariya a Ingila - Vieira


Kocin Crystal Palace Patrick Vieira ya bayyana cewa akwai bukatar a kara tashi tsaye wurin kawar da nuna wariyar launin fata da ake yi wa 'yan wasa.


Yana martani ne bayan da aka fitar da sanarwar cewa za a rage dabi'ar saka gwuiwa daya a kasa gabanin fara wasannin kakar bana, wata alama da ke nuna adawa da nuna wariya.


An takaita hakan in banda a manyan wasannin gasar Premier League da kuma wasannin karshe na kofin FA da kuma Carabao.


Sai dai tsohon kyaftin din Arsenal kuma mai horar da Crystal Palace Patrick Vieira ya ce ana wasa da muhimmancin da adawa da nuna wariyar ke dashi, don a cewarsa abu ne da ya kamata a karfafa yi a maimakon yi masa rikon sakainar kashi.


''Yana da muhimmanci a cigaba da saka kafa a kasa don nuna adawa da nuna wariya don duk muna adawa da hakan.''


Yaki ne da zai dauki tsawon lokaci ana yi a don haka dole mu cigaba da saka gwuiwa a kasa," in ji Vieira.


A watan Fabrairun 2021 ne dan wasan gaban Crystal Palace Wilfried Zaha ya daina dabi'ar saka gwuiwa a kasa, inda ya kafa hujja da cewa yin hakan bai sauya komai ba don har yanzu da dama daga cikinsu na fuskantar wariyar launin fata.


An samo dabi'ar ne daga wani dan wasan kwallon zari rugar Amurka Colin Kaepernick a ranar 1 ga watan Satumban 2016, don nuna adawa da wariyar launin fata da cin zarafin da yan sanda ke yi wa bakake a kasarsa.

(BBC HAUSA)

9 views0 comments
bottom of page