top of page
  • Writer's pictureArtv News

An yabawa maniyyata aikin Hajin bana na Kura da D/Kudu bisa jajircewarsu wajen halartar Bita

Daga Nura Ahmad Dakata

Da yake gabatar da jawabi a yayin zyarar, daraktan sashen ilmantawa da wayar da kawunan alhazai na hukumar alhazai ta kano, Alhaji Nuhu Garba Salihu Dambatta, ya ja hankalin aniyyatan kan kiyayewa da dokokin kasa mai tsarkiMalam Nuhu Garba Salihu Dambatta ya kuma yi amfani da damarsa wajen yabawa maniyyatan bisa kokarinsu da jajircewa wajen halartar taron bitar a koda yaushe kuma a kan kari cikin tun a shekarun biyun da suka gabata


Haka kuma daraktan ya shawarci maniyyatan kan cewa su lura da wadanda zasu yi muamala dasu musammam a lokacin da suke bukatar canja kudin guzirinsu wanda za a basu a dalar amurka don karsu fada hannu yan damfaraShi ma da yake nasa jawabin, shugaban kwamitin malaman bita ana Jahar kano, Sheikh Muhammad Haroon Ibn Sina, wanda ya samu wakilcin sakataren kwamitin, Malam Usman Mustapha Madabo, yabawa maniyyatan yayi bisa cikakken hadin kai da goyon baya da suke bayarwa tare da fatan zasu dore da yin hakan har zuwa kasa mai tsarki.


Ya kuma tayasu murna bisa zabarsu da allah yayi don su ziyarci dakinsa mai alfarma a wannan shekara duk kasancewar dubban mutane sun nemi zuwa amma hakansu bai cimma ruwa ba


A jawabinsa, babban mai baiwa gwamna shawara kan harkokin hukumar alhazai, Malam Salisu Ahmad Bandirawo, addu’a yayi kan Allah ya sanya ayi aikin Haji karbabbe kamar don samun yafewar zunubai kamar yadda Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wa sallam ya bayyana ga duk wanda ya yi hajin karbabbiya


Ya shawarcesu da su dauki dabi’ar hakuri da juna a lokacin aikin haji, kasncewar zasu hadu da mutane masu halaye da dabi’u daban-daban

47 views0 comments
bottom of page