top of page
  • Writer's pictureArtv News

An wayi gari cikin karanci da tsananin tsadar Burodi a Najeriya


’Yan Najeriya na fama da karanci da kuma tsananin tsadar burodi bayan masu gidajen burodi

sun fara yajin aiki a fadin kasar.


A safiyar Alhamis Babbar Kungiyar Masu Gidajen Burodi ta fara yajin aiki, saboda abin da ta kira tashin gwauron zabon kayan hada burodi.


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa tun kafin fara yajin aikin nasu da zai dauki tsawon kwana hudu, ’yan Najeriya ke ta bayyana damuwa, bayan a wasu wuraren an ninka farashinsa.


Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Burodi da Dangoginsu ta Kasa, Emmanuel Onuorah tare da Kakakin kungiyar, Babalola Thomas sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 cikin 100 da take karba na bunkasa noman alkama daga hannunsu.


Sun kuma bukaci Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta rage yawan kudin da mambobin kungiyar ke biya na Naira 154,000 kan jinkirin sabunta lasisi.


Sun kuma bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya rika ba wa masu kamfanonin burodi rancen da aka ware wa matsakaita da kananan masana’antu.


Haka kuma suna kira da a’a dakatar da yawan hukumomin da ke sanya ido kan harkokin sana’ar burodi.

16 views0 comments
bottom of page