Artv News
An naɗa tsohon shugaban Al-Shabab a matsayin minista a Somaliya

An naɗa tsohon mataimakin shugaba kuma mai magana da yawun ƙungiyar al-Shabab ta Somaliya a matsayin ministan ƙasar.
An zaɓi Mukhtar Robow a matsayin ministan harkokin addini a sabuwar majalisar ministoci ta Somalia.
Ƴa daɗe a cikin ɗaurin talala na tsawon shekaru hudu bayan da aka kama shi a lokacin a mulkin tsohon shugaban ƙasar, saboda ya shirya wata ƙungiyar ƴan bindiga.
An kuma zarge shi da rashin yin watsi da tsattsauran ra'ayi.
An kashe fiye da mutum 20 a lokacin da tashin hankali ya ɓarke bayan an kama shi.
Ya bar ƙungiyar al-Shabab a shekarar 2015 inda yake kafa hujja kan bambancin aƙida, sai ya buɗe tasa ƙungiyar ƴan bindigar.
Akwai lokacin da Amurka ta sanya sunansa a jerin waɗanda ake nema saboda ayyukan ta'addanci.
Ta yi tayin bayar da dala miliyan biyar ga duk wanda ya kama shi, amma an yi watsi da wannan batu a shekarar 2017.
Naɗa shi a matsayin ministan harkokin addini yana iya ayyana yaƙin adawa da aƙidar al-Shabab.
Amma wasu suna ganin kamar an yi hakan ne don rufe laifukan da ya yi lokacin da yake da alaƙa da ƙungiyar al-Qaida.
Ƙungiyar al-Shabab, wadda ke adawa da gwamnatin Somaliya da ke samun goyon bayan ƙasashen duniya, na kai hare-hare akai-akai a Somaliya.
Sannan takan kai hari har a kasashen da ke maƙwabta da ita.
BBC Hausa