Artv News
An ja hankalin maniyyatan jahar Kano da su yi hattara da 'yan damfara
Daga Nura Ahmad Dakata

araktan wayar da kai da ilmantar da ilamantarwa na hukumar kula da jin dadin alhaai ta kano, Alhaji Nuhu Garba Salihu Dambatta, shi ne yay jan hankalin yayin da ya jagoranci jami'an hukumar zuwa cibiyoyin bita na Rogo, Karaye da kuma Gwarzo
Alhaji Nuhu Garba Dambatta, yace fadin hakan ya zama wajibi , bisa la’akari da ganin cewa mafiya yawan maniyyatan na bana sababbin alhazai ne wadanda basu da gogrwa kan harkokin aikin haji

Yace hukumar na yin iya bakin bakin kokarinta wajen daukar matakan da suka wajaba don kare alhazan daga fadawa hannun muyagun mutane, don haka ya jaddada bukatar da ake yi musu na tuntubar jami’an alhazai na kananan hukumominsu ko kuma duk wani wanda suka tabbatar jami’in hukumar ne domin yi musu jan gora kan duk wani abu da ya shige musu duhu.
Malam Nuhu Garba Dambatta, yayi amfanu da taron wajen yabawa maniyyatan kananan hukumomin na Rogo, Karaye da Kuma Gwarzo, bisa yadda suka kasance musu bin doka da kuma jajircewa wajen halartar bitar inda yay fatan zasu dore da yin hakan har a can kasa mai tsarki
A nasa jawabin, baiwa gwamnan Jahar kano shawara kan harkokin hukumar, Alhaji Salisu Ahmad Bandirawo, fata yayi hakurin da maniyyatan suka yi har tsawon shekaru biyu suna jiran zuwa aikin hajin, ya sanya sus amu haji karbabbiya
Alhaji Salisu Bandirawo yayi kira ga maniyyatan da su kasance cikin nutsuwa a lokacin da aka kra su domin tafiya zuwa kasa maitsarki, inda ya jaddada cewa babu wanda za a bari a cikinsu ba tare da an tafi da shi zuwa kasa mai tsarkin ba matukar dai ya cika dukkanin sharuddan da hukumomi suka gindaya masa
A nasa bangaren, sarkin tsaftar kano, Alhaji Jamilu Ahmad Gwarzo, ya shawarci maniyyatan dasu kiyaye da tsaftar jikinsu da ta zuciyarsu domin samun ibada karbabbiya
Sauran wadanda suka gabatar da jawabi a yayin taron, sun hada da Sakataren kwamitin bitar alhazai na Jahar kano, Malam Usman Mustapha Madobo da da daraktar kula da sashen adashin gata, Jajiya Jamila Umar da dai sauransu.