Artv News
An gano hodar ibilis ta naira biliyan 193 a wani gida a Lagos

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta gano tare da ƙwace kilogiram 1,855 na hodar ibilis da adadin kuɗinta ya kai naira biliyan 194 a wani rumbun ajiya da ke wani gida a Lagos.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, NDLEA ta ce wannan kame shi ne mafi girma da ba a taɓa yin irinsa ba a tarihin ƙwace ƙwayoyi a ƙasar.
An samu muggan ƙwayoyin ne a wani rumbun ajiya da ke wani gini cikin wani rukunin gidaje da ke yankin Ikorodu a cikin birnin Ikkon.
“An kama koken ɗin da darajarsa a kasuwa ta kai dala 278,250,000 wanda ya yi daidai da N194, 775,000,000,” in ji sanarwar.
NDLEA ta ce a yayin samamen da aka shirya shi tsaf ta hanyar tattara bayanan sirri da aka shafe kwana biyu ana tattarawa a unguwanni daban-daban na Lagos, an kama wasu manyan dilolin koken huɗu ciki har da wani ɗan ƙasar Jamaica, da kuma manajan gidan ajiyar.
Sanarwar ta ambaci sunayen mutanen da shekaru da ma jihohin da suka fito, kuma ta ce dukkansu suna cikin mambobin ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa da hukumar NDLEA take bibiyarsu tun 2018.
An kai saamen ne a ranar Lahadi 18 ga watan Satumba, a gida mai lamba 6 kan titin Olukuola a rukunin gidaje na Solebo a unguwar Ikorodu.
Su kuma dillalan ƙwayar an same su a otel daban-daban da suke samun mafaka a birnin na Ikko daga tsakanin ranar Lahadi zuwa Litinin.
Binciken farko-farko ya nuna cewa an kama ƙwayoyin mafi illa a wannan rumbun ajiyar inda dilolin ke shirin sayar da su ga masu saye a Turai da Asiya da sauran sassan duniya.
An same su ne a cikin manyan akwatuna 10 da durom 13
Shugaban NDLEA Buba Marwa, ya yaba wa jami’an hukumar da dukkan jami'an tsaron da suka taimaka wajen binciken ciki har da na hukumar hana fataucin ƙwayoyi ta Amurka US-DEA.
“Wannan samame gagarumar nasara ce kan masu safarar miyagun ƙwayoyi da ba a taba samun irinta ba a tarihi.
"Kuma babban gargaɗi ne da ke nuna cewa dukkan masu safarar ƙarshen su ya zo idan har ba su gane cewa salon ya sauya ba," in ji Buba Marwa kamar yadda sanarwar ta ambato shi yana cewa.
(BBC Hausa)