Artv News
An dawo da jigilar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna bayan harin 'yan bindiga

Jiragen kasa sun soma jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna karon farko tun bayan hare-haren da 'yan bindiga suka kai kan wani jirgin kasa a watan Maris din da ya gabata.
Jirgin kasan farko ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja ranar Litinin din nan da misalin takwas na safe inda ya isa tashar Iddu da misalin karfe 10 da rabi.
Kazalika jirgin Abuja zuwa Kaduna ya tashi bayan karfe tara na safe.
Wakilin BBC Hausa da ya je tashar jirgin da ke Abuja ya ce mutanen da suka shiga jirgin ba su da yawa.
Wasu daga cikin fasinjojin sun shaida masa cewa hakan ba ya rasa nasaba da yadda hukumomi suka rika daga ranar sake dawo da jigilar jiragen kasan.
Bayanan hoto,Ba a samu fasinjoji da yawa a tashar jiragen kasan ba
Tun da farko Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya ce ya ba da umarnin tura jami'an tsaro ɗauke da makamai don ƙarfafa matakan tsaro a sufurin jirgin ƙasa da zai dawo bakin aiki daga Abuja zuwa Kaduna.
Rundunar ta ce ta tura jami'anta na sashen 'yan sandan kwantar da tarzoma da sashen 'yan sanda masu aiki da karnuka da na ofishin tattara bayanan sirri da sashen kula da ababen fashewa, sai kuma rundunar 'yan sandan kula da sufurin jirgin ƙasa don fara wannan jigila.
Yanzu dai hukumomi sun ce sun tura ƙarin jami'an tsaro da kayan aiki don ci gaba da sufurin jirgin ƙasan na Abuja.
Rundunar 'yan sandan ƙasar a cikin wata sanarwa da ta wallafa a ranar Lahadi ta ce an tura jami'an nata ne zuwa manyan tasoshin jirgin da cikin tarago-tarago na jiragen da ke bin hanyar Abuja zuwa Kaduna don tabbatar da tsaron fasinjoji da dukiyarsu har ma da ɗaukacin harkar sufurin, a ƙoƙarin kare aukuwar duk wani abin ƙi nan gaba.
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasar NAN ya ambato Hukumar Kula da Sufurin Jirgin ƙasan Najeriya na cewa gwamnati ta yi asarar sama da naira miliyan 113 a tsawon wata takwas da jiragen suka shafe ba sa aiki.
Haka zalika ta ce ta ɗauki ƙwararan matakan tsaro don hana sake aukuwar ƙazamin harin ranar 28 ga watan Maris, ciki har da ɓullo da tsarin amfani da lambar zama ɗan ƙasa ta NIN kafin a sayar wa matafiyi tikitin jirgi.
A makon da ya gabata ne dai ministan sufurin jirgin ƙasa ya jagoranci 'yan jarida da sauran jami'an gwamnati zuwa Kaduna, don gwajin tsarin da aka ɗauka kafin dawo da sufurin jirgin ƙasan gadan-gadan daga safiyar ranar Litinin.
Tuni hukumar kula da sufurin jirgin ƙasa ta Najeriya ta buɗe kafar sayen tikiti ta shafinta na intanet, don fara jigilar da aka dakatar tsawon wata takwas a baya.
A ƙarshen watan Maris ɗin 2022 ne, hukumomin Najeriya suka dakatar da sufurin jirgin ƙasan, bayan mummunan harin da 'yan fashin daji suka kai wa ɗaya daga cikin jiragen mai ɗauke da ɗaruruwan fasinjoji a kusa da garin Katari cikin jihar Kaduna.
A yayin harin, 'yan bindiga sun fasa nakiyoyi tare da buɗe wuta kan fasinjoji, abin da ya yi sanadin mutuwar wasu, wasu da dama kuma suka ji raunuka, sannan 'yan fashin suka sace fiye da mutum sittin.
Daga bisani dai, an riƙa sako fasinjojin rukuni-rukuni, inda aka saki rukunin ƙarshe da ya ƙunshin mutum 23 a farkon watan Oktoba.