Artv News
An binne gawar Sarauniya - Iyalanta

Iyalan gidan Sarautar Birtaniya sun ce sun binne gawar Sarauniya Elizabeth ll a wata kebantacciyar jana'izar da suka gudanar a fadarta da ke Windsor.
A wata sanarwa da suka fitar a shafinsu na yanar gizo, sun ce sun binne ta ne tare da mijinta Yarima Philip, a hubbaren 'King George VI Memorial' da ke cocin St George 'Yayanta da jikokinta ne kadai suka halarci binne gawar tata.
A wannan cocin ne dai aka binne mahaifinta Sarki George VI, da mahaifiyarta, da kuma kanwarta gimbiya Margaret