Artv News
An ɗage shari'ar Sanata Ekweremadu zuwa watan Oktoba

An ɗage sauraron shari'ar ɗan Majalisar Dattawa ta Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice, zuwa watan Oktoba bisa zargin da ake yi musu na yunƙurin yunkurin cire sassan jikin mutum a Birtaniya.
Ana tuhumar sanatan mai shekara 60 da matarsa 'yar shekara 55 da yin safarar wani matashi mai shekara 21 daga Najeriya zuwa Birtaniya.
Zama na gaba da kotun za ta yi shi ne a ranar 31 ga watan Oktoba, amma sauraron ƙara da gabatar da shaidu a shari'ar sai watan Mayu na shekarar 2023.
Masu shigar da ƙara sun yi iƙirarin cewa mutanen sun kai matashin Birtaniya ne don a cire masa ƙoda da zimmar a saka wa 'yarsu.
A ci gaba da sauraron ƙarar a ranar Alhamis, Beatrice wadda aka ba da belinta, da kuma na ukunsu mai suna Obinna Obeta sun bayyana ne ta bidiyo a kotun Old Baily.
An ce matashin ya ƙi amincewa ne bayan an yi masa gwaji a asibitin Royal Free da ke Hampstead a birnin Landan.
Haka nan an zargi ɗan majalisar da matarsa da tafiyar da rayuwar mutumin a matsayin bawa kafin ya gudu tare da kai ƙara a ofishin 'yan sanda na Staines da ke Surrey.
An kama ma'auratan ne a Filin Jirgi na Heathrow ranar 21 ga watan Agusta bayan sun sauka daga ƙasar Turkiyya.
Sabon alƙali ne zai saurari ƙarar
A zaman na ranar Alhamis, waɗanda ake zargi sun bayyana ta bidiyo daga gidajen yarin da ke Wandsworth da kuma Belmarsh.
Ana zargin matar Ekweremadu da Mista Obeta da haɗa baki wajen shirya balaguron wani mutum bisa niyyar su cuce shi.
Yayin zaman kotun, ba a nemi waɗanda ake zargi su amsa laifinsu ba kuma sun yi magana ne kawai don su bayyana sunayensu.
Mai Shari'a Richard Marks QC ya ce wani sabon alƙali ne daga Babbar Kotu zai ci gaba da sauraron shari'ar a ranar 2 ga watan Mayun 2023.
Ya yi hasashen cewa shari'ar ba za ta wuce mako uku zuwa huɗu ba. Amma za a yi wani zaman a ranar 31 ga watan Oktoba.
Alƙalin ya ci gaba da bai wa Beatrice beli amma ya ba da umarnin a mayar da Ekweremadu da Obeta a gidan yari.
(BBC HAUSA)