top of page
  • Writer's pictureArtv News

Amurka ta lashi takobin taimaka wa Ukraine wajen gurfanar da Rasha


Ministan Shari’ar Amurka Merrick Garland, ya lashi takobin taimaka wa gwamnatin Ukraine wajen shigar da karar Rasha da ake zargi da aikata laifukan yaki a kasar ta Ukraine. Ministan Shari’ar na Amurka ya bayyana haka a wata ziyarar ba-zata da ya kai Ukraine a jiya Talata, inda ya jaddada goyon bayan Amurka ga al’ummar Ukraine da suka tsinci kansu cikin wani hali saboda mammayar Rasha.

Tuni Mista Garland ya sanar da kafa wani kwamiti karkashin shugabancin Eli Rosenbaum, kwararran lauyan nan da ya jagoranci Amurka har ta yi nasarar gano tare da tasa keyar ‘yan Nazi da suka aikata laifukan yaki.

RFI ta rawaito cewa, Garland ya ce, Amurka da sauran kasashen duniya sun ga hotuna masu tayar da hankula da ke nuna irin girmar barnar da Rasha ta yi a Ukraine, yana mai cewa, babu maboya ga miyagun mutane kuma za a gurfanar da su.

Ministan Shari’ar dai ya yada zango ne a Ukraine akan hanyarsa ta zuwa birnin Paris domin halartar wani taro tsakanin Amurka da kasashen Turai kan lamurran da suka shafi shari’a da kuma harkokin cikin gida.

Kusan watanni hudu kenan da fara yakin Ukraine, yayin da gwamnatin kasar ta bayyana cewa, ta tattara dubban hujjoji kan zargin da ake yi wa Rasha na aikata laifukan yaki a kasar.

10 views0 comments
bottom of page