top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ambasada Muhammad Abba Dambatta ya zama sabon Sarkin noman Dambatta

Daga Nura AhmadSa’in Bichi Hakimin Danbatta, Alhaji Isyaku Wada Waziri, ya nada Sakataren zartarwa na hukumar kula da jin alhazai na Jahar Kano, Ambasada Muhammad Abba Dambatta a matsayin sabon Sarkin noman yankin karamar hukumar Danbatta.


Da yake gabatar da jawabi a yayin bikin wanda aka gudanar a Kofar fadarsa, Hakimin na Dambatta, yace ya ga dacewar ba shi sarautar ce domin karfafa masa gwiwa wajen ci gaba da taimakawa jama’a ta fannin harkokin noman da yake yi a yankin.Yayi kira ga sabon sarkin noman da ya kara zage damtse wajen kyautatawa jama’a da kuma kawo ci gaba mai dorewa da yake yi a karamar hukumar, wanda yace su kuma a nasu bangaren na iyayen kasa zasu ci gaba da ba shi shawarwarin da suka dace da nufin cimmam burin da aka sanya gaba.


Hakimin ya kuma godewa Ambassada Muhammad Abba Dambatta bisa yin amfani da damar da ya samu a fannin gwamnati, wajen samawa matasa ayyukan yi da taimakawa marayu da iyayensu da masu bukata ta musammam da sauran marasa galihu dake cikin al’uma a yankin da ma Jahar Kano baki baki dayaA nasa jawabin kamala bikin nadin, Sarkin noman Danbatta, Ambasada Muhammad Abba Dambatta, ya godewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa kirkirar sababbin masarautu da ya yi wanda a sanadiyyar hakan ce ta sanya ya kai ga wannan matsayi.


Haka kuma Dambatta ya godewa Mai Martaba Sarkin Bichi da Hakimin na Dambatta, Alhaji Isyaku Wada Waziri bisa karrama shi da yayi wajen ba shi sarautar ta sarkin noman yankin, inda yace farin cikinsa ba zai taba musaltuwa ba bisa wannan karamci da yayi masa.


Sauran wadanda aka nada a yayin bikin, sun hada da Dan Iyan Danbatta da Zanna da Ajiya da kuma Fagacin Dambatta.


Taron ya samu halatar masu rike da sarautun gargajiya na yankunan kananan hukumomi da dama da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da kuma sauran ‘ya uwa da abokan arziki.

26 views0 comments
bottom of page