Artv News
Ambaliyar ruwa: Majalisar zartarwa ta Kano ta amince da rusa gine-gine a Kwarin Gogau da K/Kwari

Majalisar zartaswa ta jihar Kano ta amince tare da ba da umarnin yin alama tare da rushe duk wasu gine-ginen da aka gina a rafin Kwarin Gogau a cikin babban birni. Har ila yau, an yi alamun rusa gine-ginen da aka yi kan magudanun ruwa a ciki da kewayen Kasuwar Kantin Kwari da nufin kawar da duk wani cikas da ke kawo cikas ga wucewar ruwa a kasuwar Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron majalisar zartarwa na mako-mako, wanda aka gudanar a zauren majalisar zartarwa da ke gidan gwamnatin Kano. Da suke Karbar Rahoton kwararrun kan Kasuwar Kanti Kwari kwamishinonin ayyuka Injiniya Idris Wada Saleh da na Muhalli, Dokta Kabiru Ibrahim Getso, majalisar ta kuma ba da umarnin a cire duk wasu gine-gine na wucin gadi da aka dora a saman magudanan ruwa a cikin kasuwar da kewayen nan take. Majalisar ta kuma yanke shawarar kawar da duk magudanan ruwa da suka toshe a kasuwar da kewaye da kuma kwashe kayayyakin gini da aka jibge kan layukan magudanar ruwa a kasuwar