top of page
  • Writer's pictureArtv News

Al-Nassr ta Saudiyya na zawarcin Ronaldo, Bayern Munich na son Rice


Kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudiyya ta yi wa dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, tayin kwantiragin shekara uku a farashin da ya kai fam miliyan 186.


Bayern Munich ta bi sahun takwarorinta wajen zawarcin dan wasan tsakiya na West Ham da Ingila, Declan Rice, mai shekara 23.


Tottenham ba ta kammala tattaunawa da kaftin din Ingila kuma dan wasan gaba Harry Kane ba kan sabon kwantiragi, yayin da kwatiraginsa na yanzu zai kare a shekarar 2024. Dole Spurs ta bai wa dan wasan, mai shekara 29, wani kwantiragi da ba kasafai suka saba ba kafin ya amince.


Manaja Erik ten Hag, ya bukaci Manchester United su yi kokarin maye gurbin Ronaldo idan an bude kasuwar saye da musayar 'yan wasa a watan Janairu mai zuwa, bayan ficewarsa daga kungiyar.


Manchester United ta fara fitar da jerin 'yan wasan da take ganin za su maye gurbin Ronaldo, cikinsu har da dan wasan PSV da Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 23, da kuma dan wasan gaba na Portugal da AC Milan Rafael Leao, mai shekara 23.


Liverpool ma ta fara shirin kashe makudan kudade domin sayo 'yan wasa a watan Janairu, duk da halin rashin tabbas din da kulub din ke ciki kan wanda zai mallake shi.


An tsere wa Manchester United a fafutikar daukar dan wasa tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund.


Kwamishinan wasannin Leagu Don Garber, ya tabbatar da yawan manyan kungiyoyi a Amurka sun nuna sha'awar daukar dan wasan gaba na Argentina Lionel Messi, mai shekaru 35, idan kwantiraginsa da kungiyar Paris St-Germain ta kare a kakar wasan da ke karewa.


Dan wasan Barcelona mai shekara 19, kuma na bayan Sifaniya Alejandro Balde, ya bayyana cewa ya na sha'awar wata rana ya buga wasa karkashin kungiyar Manchester United baya ga wasan La Liga da ya ke yi.


Tottenham na duba yiwuwar dauko dan wasan Juventus na tsakiyar Amurka Weston McKennie, mai shekara 24, bayan kammala gasar cin kofin duniya.


West Ham da Everton sun bi sahun wasu kungiyoyi na son dauko dan wasan Colombia winger Jhon Duran, mai shekra 18 daga Chicago Fire, su ma kungiyoyin Liverpool na zawarcin dan wasan Manchester United .


Leeds United, Everton, West Ham da Leicester City na daga cikin kulub din da ke son dauko dan wasan tsakiya na Senegal Boulaye Dia. Mai shekara 26 a yanzu ya na matsayin aro a kungiyar Salernitana daga Villarreal.


Leicester, Brighton da Nottingham Forest na son dauko dan wasan Huddersfield kuma na tsakiyar Faransa Etienne Camara, mai shekara 19.


Manajan Barcelona Xavi ya ce a kashin kan sa ya yi magana da dan wasan Palmeiras Endrick mai shekara 16 domin ya amince shiga kulub din La Liga.

BBC

16 views0 comments
bottom of page