top of page
  • Writer's pictureArtv News

2023: Gawuna/Garo Akan Mizani


Daga Aminu Dahiru


A kalla yau saura wata bakwai ai zaben gwamnoni. Zabe shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya zai gudana cikin ikon Allah 25 ga watan faburairu, a yayinda zaben gwamnoni da yan majalisar jiha zai gudana 11 ga watan maris na shekarar 2023.


Har izuwa yanzu dai ba a kada gangar siyasa ba a hukumance dan bawa ‘yan takarkaru damar tallata hajarsu. Duk da haka akwai wata tambaya mai matukar mahimmanci da ke tsimayin amsa daga wajen Kanawa. Wannan tambaya ita ce: waya ya cancanta da ya cigaba da gudanar da al’amuran wannan jiha ta Kano mai albarka bayan wa’adin mulkin Baba Ganduje ya kare a shekarar 2023?


Akwai abubuwa da yakamata a yi la’akari da su kafin bada wannan amsa. Duk wani akili wanda ya kai shekarun zabe yakamata ya fahimci daga inda ake kuma ina za a je. Yakamata a yi duba na tsanaki kan nasarori da gwamnatin Jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar APC ta samu a cikin shekaru bakwai da wasu watanni da suka gabata da matakin da jihar take kafin wannan lokaci da kuma yanzu.


Bayan haka akwai bukatar dora kowane tantakara a mizani dan fahimtar irin amfani da yake da shi ga al’ummar wannan jiha da kudire-kudire da yake da su dan cigaba da inganta rayuwar Kanawa musamman matasa da mata.


Zaben 2023 zabe ne na goyan bayan cigaba ko akasin haka. Zabe ne da zai maida hankali wajen mu’amalar dan takara da yanda yake jibintar al’amuran al’ummarsa da biyyarsa ga shugabanni da kuma irin kauna da yake da ita ga wannan jiha tamu da ake wa lakabi da cibiyar kasuwanci.


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi hangen nesa da zufin tunanin da ya zabawa al’ummar wannan jiha mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da tsohon kwamishina na kananan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo a matsayin dan takarar gwamna da kuma mataimakinsa a kakar zabe mai zuwa a karkashin inuwar Jam’iyyar APC.


Dr. Nasiru Yusuf Gawuna gogaggen ma’aikacin gwamnati ne kuma dan siyasa wanda yake da halin dattako. Yayi shugaban karamar hukuma har sau biyu. Tsohon kwamishina ne, har ila yau kuma mataimakin gwamna ne. Babu wani lungu ko sako na gwamnati da zai shige masa duhu.


Juriya da hakuri da hangen nesa da wadatar zuci su ne kalmomin da za ka iya siffanta Gawuna da su.


Gogewarsa a fannin gudanarwa da irin gudumawar da ya bayar ga wannan jiha tun lokacin da ya zama mataimakin gwamna manuniya ce cewa babu wani wanda ya fi cancanta da ya zama gwamna a shekarar 2023 fiye da wannan bawan Allah.


Alhaji Murtala Sule Garo tsohon kwamishinan kanan hukumomi ne na wannan jiha, matakin da ya rike tsawan kimanin shekaru bakwai da wasu watanni. Garo cikakken jagorana ne. Jagaba ne a wajen fannin siyasa wannan jiha ya gina matasa. Allah ne kawai yasan adadin matasa da mata da ya tallafawa wanda a yanzu haka suna tsaye akan kafafuwansu.


Ana masa laqabi da kwamande ne domin jajircewar sa wajen ganin anyi abinda ya dace a lokacin daya dace, babban burinsa shi ne gina matasan wannan jiha birni da kauye.


Tabbas idan ka dora Dr. Nasiru Yusuf Gawuna Gawuna da Murtala Suke Garo akan mizani za su rinjayin duk wasu ‘yan takarkaru. Dalili, kuwa shi ne babbar manufarsu it ace gina al’ummar wannan jiha musamman matasanta da mata dan cigaba mai dorewa a Jihar kano.


#Gawuna/Garo2023

16 views0 comments
bottom of page