top of page
  • Writer's pictureArtv News

2023: Bai Halatta Jam’iyyu Su Karbi Gudunmawar Da Ta Wuce Miliyan 50 Ba — INEC
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gargadi ’yan takara da ma jam’iyyu da kada su kuskura su karbi ko su bayar da gudunmawar da ta wuce ta Naira miliyan 50 a babban zaben 2023 mai zuwa.


Gargadin na kunshe ne a cikin wani kundin ka’idojin shirya gangami, yakin neman zabe da samar da kudaden da ’yan takara za su kashe yayin zaben 2023, wanda hukumar ta fitar a Abuja ranar Juma’a.


A cewar INEC “Mafi girman gudunmawar da daidaikun mutane ko kungiyoyi za su iya ba dan takara ko jam’iyyu ita ce Naira miliyan 50.


“Bai halatta jam’iyyu su karbi gudunmawar tsabar kudi ko ta kayan aikin da ta wuce Naira miliyan 50 ba, sai dai idan za a bayyana wa hukumarmu daga inda kudaden suka fito.


“Bugu da kari, za a iya ba ’yan takara gudunmawar yakin neman zabe ne kawai kwana 150 kafin ranar zabe.”


Kundin ya kuma ce abin da jam’iyya za ta kashe ya kunshi duk wasu kudade ko kayan aiki da jam’iyya ko dan takara zai kashe, kuma dole ne a wallafa su kafin ranar zabe.


INEC ta kuma ce kudaden da jam’iyyu za su kashe hawa uku ne; na masu neman tsayawa takara da zabukan fid-da gwani, na ’yan takara da kuma gudanar da zaben, sai kuma ’yan kunji-kunji a ranar zaben.


Kundin ya kuma ce kudaden da ake magana a kansu sun hada da na kararrakin da za a shigar a kotu, abubuwan da za su biyo bayan zabe da kararrakin bayan zabe da kuma na sake hada kan ‘yan jam’iyya bayan kammala zaben.

0 views0 comments
bottom of page