Artv News
Ɗan Sule Lamido ya zama ɗan takarar gwamnan Jigawa a PDP

Alhaji Mustafa Lamido, ɗan tsohon gwamna Sule Lamido na Jigawa, ya zama ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Jami’in kula da masu kada kuri’a na zaben fidda gwani, Malam Isah Ahmed, ne ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana sakamakon zaben yau Laraba a Dutse.
Ahmed ya ce, Mustafa ya samu ƙuri’u 829 daga cikin kuri’u 832 da aka kaɗa, inda ya ƙara da cewa, Alhaji Saleh Shehu ya zo na biyu a zaɓen wanda bai samu ƙuri’a ko ɗaya ba.
Ya taya wanda ya lashe zaben da wakilan jam’iyyar da kuma ƴaƴan jam’iyyar murna bisa yadda suka gudanar da zaben ba tare da ya cikas ba.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Babandi Ibrahim, ya ce jam’iyyar za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen gabatar da sahihin dan takarar kujerar gwamna a jihar, wanda zai taimaka wajen dawo da martabar jihar.
Mustafa ya nuna farin cikinsa da nasarar da ya samu.
“Na amince da wannan nasara da na samu kuma zan yi kasance mai gaskiya tawali’u, kunya da azama,” in ji shi.
Ya bayyana taron a matsayin mai cike da tarihi.
“Yayin da muka shiga mataki na gaba na yaƙin neman zabe, ina rokon ku da ku amince da ni, ku yi aiki da ni, ku yi yaƙin neman zaɓe yadda ya dace kuma ku zaɓe ni domin mu sake ciyar da jihar mu gaba don haka ya kamata al’umma su fito ƙwansu da kwarkwata don zaɓar PDP.
“Ina kira gare mu da mu guji siyasar rarrabuwar kawuna da rashin haɗin kai. “Ga sarakunanmu da dattawanmu, ina girmama su sosai kuma zan riƙa tuntuɓar su akai-akai kan batutuwan da za su taimaka wajen ciyar da jiha gaba.
Na yi alƙawarin yin yaƙin neman zaɓe cikin lumana, saboda haka ina buƙatar goyon baya da addu’o’in ku,” inji shi.
Jaridar Solacebase ta ce Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa ɗaya daga cikin masu neman tsayawa takara Alhaji Adamu Bashir ya sanar da janyewarsa ƴan sa’o’i kafin a fara zaben fidda gwanin.