top of page
  • Writer's pictureArtv News

Ƴan bindiga sun ba sojoji wa’adi su fice yankin kudu maso gabashin Najeriya

Ƴan bindigar da ake zargi sun kashe ɗan majalisar jihar Anambra a kudancin Najeriya Okechukwu Okoye, sun ba da wa’adin awa 48 sojoji su fice daga yankin na kudu maso gabashi.



Wannan wa’adin na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da aka samu a gefen kan da ƴan bindigar suka fille na ɗan majalisar, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.


Ƴan bindigar sun sace ɗan majalisar ne kuma suka kashe shi ta hanyar fille kansa da suka rataye a gefen hanya da aka gani a ranar Asabar.


Rundunar ƴan sanda a yankin a cewar jaridar ta yi watsi da barazanar inda aka ambato kwamishinan ƴan sandan Anambra Echeng Echeng na shan alwashin farautar ƴan bindigar

44 views0 comments
bottom of page